An gufanar da hukumar zaben Kamaru a gaban Kuliya

A Kamaru, wasu 'yan takara goma sha takwas, da hukumar zaben kasar, ELECAM, ta yi watsi da takardunsu na neman yin takarar shugabancin kasar, sun shigar da kara a kotun koli.

Suna zargin cewar hukumar zaben ba ta yi masu adalci ba.

A karshen makon jiya ne ELECAM ta wallafa sunayen 'yan takara 21 daga cikin 52, wadanda suka nemi tsayawa a zaben shugabancin kasar.

A ranar tara ga watan Oktoba mai zuwa ne dai za a yi babban zaben kasar ta Kamaru.