'Za mu kafa hukuma mai sassaucin ra'ayi'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mustafa Abdul Jalil

Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta 'yan tawaye a Libya, Mustafa Abdul Jalil, ya ce za a gudanar da mulkin kasar ne a karkashin tsarin mulkin dimokaradiyya na Islama.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da duk wadansu masu tsattsauran ra'ayi ba.

Ya fadi hakan ne a jawabinsa na farko a bainar jama'a a Turabulus, babban birnin kasar.

Kazalika ya ce gwamnati za ta bayar da muhimmanci ga shigar mata a dama da su cikin aiwatar da lamuran kasar.

Dubban 'yan kasar ne dai suka yi cincirindo don sauraron jawabinsa a dandalin da ke tsakiyar birnin Turabulus, inda nan ne Kanar Gaddafi kan gabatar da jawabai ga magoya bayansa.

'Zargin take hakkin bil Adama'

Sai dai a yayin da Mista Abdul-Jalil ke gudanar da wannan jawabi, kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya, Amnesty International, ta yi kira a gare ta da ta dakatar da cin zarafin jama'ar da ta ce dakarun Kanar Gadafi ke yi a kasar.

Ta kara da cewa dakarun Gaddafin na cigaba da aiwatar da laifukan da suka sabawa dokokin kasashen duniya.

Kugiyar ta ce tana da shaidun da ke nuna cewa su ma dakarun 'yan tawayen na ci gaba da cin zarafin jama'a, don haka ne ta yi kira ga gwamnati da ta dakatar da hakan.