'Tattalin arzikinmu zai bunkasa'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wen Jiabao

Firimiyan kasar Sin, Wen Jiabao ya ce tattalin arzikin kasar zai ci gaba da bunkasa a cikin wadansu 'yan shekaru da ke tafe, abin da ya ce, zai yi sanadiyar bunkasar kasashen duniya.

Mista Wen ya yi wannan tsokaci ne a wani taron bunkasa tattalin arziki da ake gudanarwa a birnin Dalian na kasar.

Wadansu kasashen dai na so ne kasar Sin ta maida hankali wajen ganin ta magance tabarbarewar tattalin arzkin da kasashen duniya ke ciki.

Sai dai Mista Wen ya ce Sin din ba ta yi tunanin yin hakan ba.

Ya ce manyan kasashen duniya, wadanda sune suka jefa tattalin arzikin duniya cikin rudani, su ya kamata su samar masa mafita.