Tarayyar Turai tace zata cigaba da tafiya da kasar Girka

Sabbin dabarun shawo kan rikin Euro
Image caption Darajar kudin na Euro na kara ja da baya

Shugabannin Tarayyar Turai sun ce zasu cigaba da tafiya da Girka duk da fargabar cewa zata kasa biyan bashin da ake binta.

Kasar ta Girka ta tabbatar wa sauran kashen Tarayyar Turan, musanmanma Jamus da Faransa cewa zata biya duk wani bashin da ake binta don ta cancanci zagaye na gaba na tallafin da za'a bata