Mutane da dama sun mutu a Iraqi

Mutane da dama sun mutu a Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai hare-haren ne a wurare daban-daban

Wasu hare-hare uku da aka nufi jami'an tsaron Iraqi sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 17, yayin da wasu 50 suka jikkata, a cewar mahukunta.

Hari mafi muni shi ne wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13, lokacin da wani bom ya fashe a cikin mota a gaban wani gidan cin abinci inda jami'an tsaro suka fi halarta.

Gwamnan yankin Babil Sadiq Rasul al-Mohannah ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a Medhatiyah da ke Kudancin Baghdad.

Tunda farko sojoji 15 ne aka kashe bayan da wani bom da aka dana a wata motar soji ya tashi a sansanin soji na Habaniya, a yammacin Baghdad.

A wani harin daban kuma, wani bom a mota ya tashi a wani wurin cin abinci a al-Hamza, wani karamin gari da ke da nisan kilomita 100 da Baghdad.

A wani lamarin daban kuma a Baghdad, wani mahari ya bude wuta kan wurin bincike na 'yan sanda a yankin Ad Hamiyah, inda ya kashe 'yan sanda biyu, sannan ya raunata wani mutum guda.