Kungiyoyin agaji sun nemi taimako don ambaliyar ruwa a Pakistan

Kungiyar samar da agaji ta kasa da kasa, Oxfam ta ce tilas ne a samarwa da miliyoyin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a kudancin Pakistan agajin gaggawa, ko kuma a samu karin wadanda za su rasa rayukansu.

A lokacin da take kaddamar da asusun bada agajin gaggawa, kungiyar Oxfam ta ce ruwan ya mamaye filaye masu yawan gaske.

Wakiliyar BBC ta ce yanzu haka dubban mutane sun fice daga gidajansu, kuma suna matukar bukatar abinci da matsugunni.

Ruwan da aka kwashe kwanaki goma ana tabkawa kamar da bakin kwarya ne ya janyo ambaliyar ruwan a lardin Sindh.

Da yawan wadanda ambaliyar ta shafa da ma suna kokarin farfadowa daga ambaliyar ruwan da aka yi bara.