Jam'iyyar ACN ta rabu biyu a Kaduna

Taswirar Najeriya
Image caption ACN ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya

A Najeriya jam'iyyar adawa ta ACN a jahar kaduna na fama da rikice-rikicen cikin gida, inda har ta kai jam'iyyar rabewa gida biyu.

Wasu shugabannin jam'iyyar bisa jagorancin shugaban jam'iyyar Barrister Muhd Musa Soba, na cewa sun kori wasu daga cikin manyan 'yan jamiyyar wadanda suka zarga da yiwa jam'iyyar zagon kasa.

Yayainda wadanda aka ce an kora kuma ke ikirarin cewa su ne da Jam'iyyar kuma har ta kai su ga bude sabuwar sakatariya.

Wannan dambarwa dai na faruwa ne a yayin da jam'iyyu a jahar, ke kokarin hada karfin su wuri guda domin tunkarar zaben kananan hukumomin dake tafe a jahar.