Kungiyar UEMOA za su yaki bazuwar makamai

Ana taron kungiyar UEMOA a Yamai Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Ana taron kungiyar UEMOA a Yamai babban birnin Nijar.

Kwamitin 'yan majalisar dokokin kasashe mambobin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma masu amfani da kudin CFA wato UEMOA, sun ce za su tallafa wajen wanzar da zaman lafiya tsakaninsu, kasancewar wasunsu na makwabtaka da Libya.

A tattaunawar da wakilin BBC, Baro Arzika a Yamai, dan majalisar dokoki kuma mamban kwamitin, Malam Abdu Jariri ya ce dole kasashen su haka karfi waje guda don yaki da bazuwar makamai sakamakon barkewar rikicin kasar Libiya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan kasar a Agadez ke nuna fargabar yiwuwar fadawar makamai a hannun bata gari.