Faransa da Jamus sun baiwa Girka tabbaci

Kudin euro Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kudin euro

Kasashen Girka da Jamus da Faransa sun dauki matakai na yin watsi da jita- jitan dake yaduwa na cewa maiyiwuwa kasar Girkan ba za ta iya biyan basussukan da ake binta ba.

Bayan wata tattaunawa ta wayar tarho, kasashen sun fidda wata sanarwa data tabbatar da cewar Girkan zata cigaba da kasancewa wani bangare na tarayyar Turai.

Mai magana da yawun gwamnatin Kasar Girkan yace Prime Minista George Papandreou da Shugaba Sarkozy da Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel sun amince da aiwatar da shawarwarin da aka dauka ranar ashirin da daya ga watan Yuli.

An kuma jaddada cewar kasar Girka na cikin tarayyar turai, sai dai mutanen kasar sun koma zanga- zanga don nuna adawa da matakan gwamnatin na tsuke bakin aljihu.