Majalisar wakilai ta Najeriya ta kafa kwamitoci

Majalisar wakilai a Najeriya ta sanar da shugabanni da mambobin da ke cikin kwamitocinta bayan sama da watanni uku da rantsar da yan majalisar na jumhuriya ta bakwai.

Kwamitocin majalisar dai suna da muhimmanci saboda su ke aiwatar da aikin sa-ido a kan yadda bangaren zartarwar ke gudanar da aikinsa.

An samu jinkirin sanar da sunayen shugabannin kwamitocin ne sakamakon zargin da ake yi cewa jam'iyya mai mulkin kasar ta nace sai an bai wa wasu daga cikin 'yan majalisar wasu muhimman mukamai bisa tsarinta na karba-karbar mulki, amma sai mafi yawan `yan majalisar suka ki amincewa da hakan.