An tuna da mamatan harin bam na Abuja

Harin bam a Abuja Hakkin mallakar hoto nta
Image caption Harin bam a Abuja

A Najeriya an gudanar da taron tunawa da wadanda suka rasu, sakamakon harin bam da aka kai a hedkwatar majalisar dinkin duniya dake Abuja.

Mutane 23 ne suka rasu a harin na ranar 26 ga watan Agustan da ya wuce, wanda kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kaiwa.

Ashirin daga cikin wadanda suka hallakar 'yan Najeriya ne.

Akwai kuma wani lauya dan kasar Norway, da kuma wasu mutanen biyu da ba a shaida ba.

Makonni ukku kenan da a kai harin, a ranar 26 ga watan Agusta, wanda kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kaiwa.

Wadanda su ka halarci taron na yau sun hada da jami'an diplomasiyya na kasashen waje da kuma na majalisar dinkin duniyar.