Obasanjo ya gana da iyalan 'yan Boko Haram

Chief Olusegun Obasanjo
Image caption Chief Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo, ya kai ziyara gidan iyalan tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, marigayi Mohammed Yusuf, da kuma gidan surukinsa Alhaji Baba Fugu Mohammed.

An zargi jami'an tsaro da yiwa mutanen biyu kisan gilla a 2009, a lokacin wani tashin hankali a Maiduguri.

Tsohon shugaban Najeriyar ya bayyana cewa, ziyara ce ta kashin kansa, kuma ya je ne domin yayi masu ta'aziyya, da kuma jin irin damuwarsu da bukatunsu, da zummar isar da su ga gwamnatin tarayya, ta yadda za a sami mafita.

Comrade Shehu Sani, na kungiyar kare hakkin dan adam ta Civil Liberty Congress a Najeriyar, shine kan gaba wajen shirya ganawar da aka yi a jiya.

Chief Obasanjo ya kuma kai wata ziyarar ba - zata a jiyan a jihar Plateau mai fama da rikici.

Babu cikaken bayani akan irin abubuwan da tsohon shugaban ya yi a lokacin ziyarar tasa.

Sai dai bayanai na nuna cewar ya gana da gwamna Jonah Jang na jahar ta Plateau.