Kasuwannin shunku sun tashi a duniya

kasuwar hannayen jari Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption kasuwar hannayen jari

Kasuwannin shunku a duniya sun tashi bayan wasu manyan bankuna biyar sunce suna daukar sabbin matakai na tunkarar rikicin kudade.

Bankunan za su samar da wasu basussuka na dalar Amurka ga wasu bankunan kasuwanci guda biyar, domin tabbatar da cewa sun samu isasssun kudaden da za su biya basukan da ake binsu akan lokaci.

Kasuwar shunku ta birnin Tokyo a ranar juma'a ta tashi, haka kuma hannayen jari a New York sun tashi a rana ta hudu a jere.