Sarkozy zai gana da jami'an Nijar

Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy

A yau ne shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy zai yi wata ganawa da wakilan gwamnatin kasar Nijar a birnin Paris, domin tattauna maganar jami'an gwamnatin Gaddafi dake gudun hijira a Nijar.

A wajen taron dai ana jin cewa hukumomin Faransan za su yiwa takwarorinsu na Nijar tayin su mika 'yan gudun hijirar na Libiya ga hukumomin 'yan tawayen NTC, kana kuma su tabbatar da cewa ba su baiwa Kanal Gaddafi mafaka ba.

Malam Musa Cangari, shugaban kungiyar Alternative Espaces Citoyens, ya ce idan gwamnatin Nijar ta bi abinda Faransa ke so, ya nuna basu kare cin gashin kan Nijar ba kuma sun yi abinda bai dace ba.