An kashe surukin shugaban kungiyar boko haram

Image caption Shugaban kungiyar boko haram

Hukumomin Tsaro a jihar Borno sun tabbatar da kisan da wasu yan bindiga suka yiwa Alh Baba Kura Fugu, babban dan surukin shugaban Kungiyar Boko Haram, marigayi Mohammad Yusuf.

Bayanai dai sun ce wasu 'yan bindiga ne suka iske marigayin a kofar gidansu dake kusa da tsohuwar Helkwatar kungiyar ta Boko Haram inda suka bude masa wuta.

Kisan ya zo ne kwanaki biyu bayan wata ziyarar jaje da tattaunawa da tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya kai gidan iyalan shugaban kungiyar ta Boko Haram da na surukin nasa Alh Baba Fugu Mohammed.

Ana zargin jami'an tsaro da yi masu kisan gilla bayan murkushe kungiyar ta Boko Haram a shekarar 2009.

An dai samu bayanai masu cin karo da juna a game da wannan kisa inda wasu yayan kungiyar ta Boko Haram suka aikewa kafafen yada labarai sakonnin cewa su ke da alhakin kisan, amma mai magana da yawun kungiyar ta Jama'atu Ahlus Sunnah lid Da'awati wal Jihad , Abu Qaqa nisanta kansu ya yi da kisan.

Wannan al'ammari dai ya dada jefa jama'a a birnin na Maiduguri cikin zullumi da rudani.