Bikin Sallar makiyaya ko Cure Salee a Nijar

Wasu rakuma suna kiwo a cikin Hamada
Image caption Wasu rakuma suna kiwo a cikin Hamada

A Jumhuriyar Nijar yau ne aka bude bikin Sallar lasar gishiri ko Cure Salee a garin Ingall na jihar Agades dake Arewacin kasar.

Bikin, wanda ake yi shekara-shekara, wata dama ce ga makiyaya daga ciki da wajen kasar ta Nijar, domin su shayar da dabbobinsu ruwan wani tafki mai gishiri na musamman, da nufin kyautata lafiyarsu.

A wajen bikin dai, makiyayan sun koka da yadda a bana ake fuskantar karancin ciyawar dabbobi a wasu sassan kasar saboda fari, amma gwamnati ta yi musu alkawarin cewa za ta dauki matakai na kare dabbobinsu.

Sai dai a bana ana yin bikin ne yayinda yankin na Arewacin Nijar ke fuskantar barazanar tsaro daga 'yan kungiyar al Qaida a yankin Magrib.