Amirka ta zargi Pakistan

Cameron Munter Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Cameron Munter

Jakadan Amurka a Pakistan Cameron Munter ya ce akwai hujjar dake alakanta daya daga cikin kungiyoyin da ke tada kayar baya a Afghanistan, wato kungiyar Haqqani da gwamnatin kasar ta Pakistan.

Mr Munter ya fadi haka ne a wata hira da wani gidan rediyo a Pakistan, inda kuma ya ce ya kamata kasarsa da Pakistan su yi aiki tare don yaki da ta'addanci.

Amurka ta ce za ta kai hari a kan kungiyar ta Haqqani a cikin Pakistan idan hukumomin kasar suka gaza daukar wani mataki a kanta.

Ana danganta kungiyar ta Haqqani da kai manya-manyan hare-hare a Afghanistan, da suka hada da musayar wuta da aka yi awa 20 ana yi a tsakiyar Kabul a makon jiya.