An kashe wasu mutane a kudancin Kaduna

Wani da aka raunata a wani tashin hankali da aka yi a jihar Kaduna Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani da aka raunata a wani tashin hankali da aka yi a jihar Kaduna

A jahar Kaduna dake Arewacin Najeriya wasu wadanda baa san ko su wanene ba sun kaddamar da wasu munanan hare hare a karamar hukumar Jaba dake kudancin jahar, inda suka kashe mutane hudu tare da raunata wasu karin tara.

Maharan sun kai hari ne a wasu gidaje guda biyu a yankin Bitaro na karamar hukumar ta Jaba bayan da jamaa suka shiga barci.

Rundunar yan sandan jahar dai ta tabbatar da afkuwar al'amarin, to amma ta ce ba ta sami nasarar kama kowa ba.

Daruruwan jamaa ne dai suka rasa rayikansu a jihar ta Kaduna , sanadiyyar rikice-rikicen da suka biyo bayan zaben shugaban kasa na watan Afriluin da ya gabata.