Zargin cin zarafin 'yan Afrika bakar fata a Libya

Wasu 'yan Afrika bakar fata a Benghazi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu 'yan Afrika bakar fata a Benghazi

Sakamakon wani bincike da BBC ta gudanar a Libya, ya nuna cewa ana zargin dakarun 'yan tawaye dake adawa da Kanar Gaddafi, da cin zarafin 'yan Afrika bakar dake ayyukan ci rani a kasar.

Binciken ya gaano cewa an tsare daruruwan mazaje 'yan Afrika bisa zargin cewa sojan haya ne da Kanar Gaddafi ya dauko.

Hakazalika an yi zargin cewa dakarun 'yan tawayen sun kutsa cikin gidajen da 'yan ciranin ke zaune, tare da sace ma su kayyakinsu da kuma yiwa maata fiade.

Shugabannin 'yan tawayen majalisar wucin gadin Libya ta NTC dai sun sha kira ga magoya bayansu da su nuna juriya, suna masu gargadin su da kada su kai hare-hare irin na daukan fansa.

Sai dai ga alama wasu daga cikin dakarun 'yan tawayen sun yi biris da wannan kira na shugabanninsu.