'Yan tawayen Libya sun sake kai hari a kan Sirte

Wani dan tawaye a Sirte Hakkin mallakar hoto none
Image caption Wani dan tawaye a Sirte

Dakarun da ke adawa da Kanar Gaddafi sun kaddamar da sabon hari a kan Sirte, mahaifar Kanar Gaddafi.

An ga bakin hayaki ya tashi lokacin da 'yan tawayen da aka wa zagi da manyan bindigogi da artileri suka yi kokarin kutsawa cikin garin.

Amma rohotannin sun ce babu wata nasarar da suka samu saboda irin turjiyar da magoya bayan Gaddafi ke nunawa.

Amma wani Kwamandan 'yan tawayen na ganin nan da dan lokaci kadan za su yi nasara.

Babu wata hayaniya a daya garin dake karkashin ikon magoya bayan Gaddafi , wato Bani Walid inda 'yan tawayen ke sake shiri bayan an fattake su a jiya.