Yarjejeniyar gudanar da zabukan Madagascar

Image caption Tsohon shugaban kasar Madagascar Marc Ravalomanan

Shugabannin siyasar Madagascar sun sa hannu a wata yarjejeniya a Antananarivo, babban birnin kasar, wadda ta share fagen gudanar da zabubuka cikin shekara daya da kuma maida kasar bisa tafarkin Demokradiyya.

Karamin ministan harkokin wajen Afrika ta Kudu ne, Marius Franzman ya shugabanci bikin sa hannu a 'yarjejeniyar a Antananarivo, babban birnin Madagascar din.

Ya fadawa wani kamfanin dillacin labarai cewa babu mutumin da zai yi ikirarin cewa shi ne ke wakiltar 'yan kasar ta Madagascar su milioyan 20, ba tare da zabe ba.

A karkashin 'yarjejeniyar kuma, an baiwa tsohon shugaban kasar ta Madagascar, Marc Ravalomanan, wanda yanzu haka ke gudun hijira a Afrika ta Kudu, damar komawa gida don a dama da shi a harkokin siyasar kasar kafin a gudanar da zabubuka.

Manny Rakotoa-Rivelo, wanda ke shugabantar tawagar gwamnatin kasar a wurin bikin sa hannu a yarjejeniyar, ya ce jam'iyyarsa tana da niyyar yin sassauci.

'Yarjejeniyar dai, wadda jam'iyyun siyasa 8 suka rattaba hannu a kanta, ta kyale Andry Rajoelin, wanda ya hambarar da Marc Ravalomanan a shekara ta 2009, ya cigaba da shugabantar kasar na rikon kwarya, har zuwa lokacin da zaa gudanar da zabe a cikin watan Maris mai zuwa.