Ziyarar Obasanjo gun Boko Haram na jan hankula

Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne

Ziyarar da tsohon shugaban Najeriya, Chif Olusegun Obasanjo ya kai gidan iyalan tsohon shugaban Kungiyar jama'atu Ahlussunna Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram, Marigayi Mohammed Yusuf da kuma gidan surukinsa, Alhaji Baba Fugu Mohammed a Maiduguri, na cigaba da jan hankalin 'yan kasar.

Tsohon shugaban ya bayyana cewa ziyarar ta kashin kansa ce, domin ya yi musu ta'aziyya da kuma jin bukatu da kuma damuwarsu, daga bisani kuma ya isar da sakonsu ga gwamnatin tarayya, ta yadda za a samu hanyar sulhuntawa.

Wasu masana harkar tsaro a kasar sun yaba da matakin da suka ce na iya kaiwa ga sulhu da kungiyar ta Boko Haram.