An sake kashe mutane a Yemen

Masu zanga-zanga a Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Yemen

Mutane akalla goma sha takwas ne aka kashe a wani sabon fada da ya barke a Yemen, tsakanin dakarun gwamnati da masu zanga zangar son ganin shugaba Ali Abdullah Saleh ya sauka daga mulki.

Wasu shaidu sun ce 'yan sanda ne suka bude wuta da bindigogi, har ma da irin makaman nan na harbo jiragen sama, a yunkurin hana dubban masu zanga zanga danganawa da fadar shugaban kasa.

Ma'aikatar tsaron kasar ta Yemen ta fada a shafinta na Intanet cewa, masu zanga zangar ne suka fara tsokanar fada, ta hanyar jefa ma su bama-baman fetur.