An nuna wasu hotunan bidiyo na Boko Haram

Shugaban kungiyar Boko Haram, marigayi Mohammed Yusuf
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram, marigayi Mohammed Yusuf

A Nijeriya, wasu hotunan video biyu da aka fitar na dauke da hoton mutumin da ake zargin shi ya kai harin kunar bakin wake a kan ginin hedkwatar Majalisar dinkin duniyadake Abuja cikin watan jiya.

Kungiyar Boko Haram dai ta ce ita ta kai harin, inda aka kashe mutane ashirin da uku.

Kampanin dillancin labarun AFP ya samu hotunan videon, inda a ciki aka nuna Muhammad Abul Barra yana rokon gafara daga danginsa cewa su fahimci dalilan da suka sha shi daukar matakin.

Wakilin BBC ya ce a hoton videon akwai kuma jawabin daya daga cikin shugabanin kungiyar ta Boko Haram, wanda ya bayyana Majalisar dinkin duniya a matsayin majalisar makirci ta duniya.

Masu aiko da rahotanni na cewa hoton video na nuna an shiga wani sabon babi a hare haren mayakan sa kai a Najeriya, inda a baya hare- haren kunar bakin wake bakon abu ne.