Amurka ta ce Pakistan na da alaka da Haqqani

Taswirar kasar Pakistan
Image caption Taswirar kasar Pakistan

Jakadan Amurka a Pakistan, Cameron Munter, yace akwai hujjar dake nuna cewa akwai alaka tsakanin daya daga cikin kungiyoyin 'yan bindiga a Afghanisitan wato Haqqani, da kuma gwamnatin kasar.

Ya kara da cewar Amurka ta yi imanin cewa kungiyar ta Haqqani ce ke da alhakin harin da aka kaiwa ofishin jakadancin Amurkan dake kasar da kuma kungiyar tsaro ta NATO a makon daya gabata.

Washington ta jima ta na matsin lamba ga Pakistan kan cewa ta kai hari kan kungiyar Haqqani dake aerwacin yankin Waziristan, amma dakarun Pakistan na cewa basu da sukunin yin hakan.

A ranar larabar da ta wuce ne dai Amurka ta yi gargadin cewa zata dauki wani mataki na kashin kanta a cikin kasar ta Pakistan, idan har hukumomin kasar sun kasa daukar mataki akan kungiyar ta Haqqani.