Ana cigaba da artabu a Sirte da Bani Walid

Dakarun 'yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun 'yan tawayen Libya

Ana ci gaba da gumurzu tsakanin dakarun dake adawa da Kanar Gaddafi da masu mara masa baya, yayinda dakarun 'yan adawar ke kokarin karbe iko da garuruwan Sirte da na Bani Wali, wadanda su ne suka rage a hannun magoya bayan hambararren shugaban kasar. Rahotanni daga Bani Walid na cewa an rika jin karar tashin bama bamai, da kuma amon bindigogi yau da safe, lokacin da dakarun Kanar Gaddafi suka rika kai hari a kan wuraren da abokan gabar su suka ja daga a wajen birnin.

Can kuma a Sirte, wani wakilin BBC ya ce sannu a hankali, dakarun dake adawa da Kanar Gaddafi na kara matsawa gaba, yayinda ake kai hare haren bam, kan wuraren da masu kare garin suka ja daga, ake kuma karbe iko da su.