Obama zai gabatar da karin haraji

Shugaban Amurka, barrack Obama Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugaban Amurka, barrack Obama

Shugaban Amurka Barrack Obama zai gabatar da wata shawara kan sabon matsakaicin haraji ga mutanen da ke samun fiye da dala miliyan daya a shekara.

Za' a sanya shawarar cikin wani shiri na dogon lokaci kan rage gibin kasafin kudi da shugaba Obama zai gabatar a gobe litinin, kuma sabon harajin zai shafi kasa da Amurkawa rabin miliyan.

Sai dai akwai yiwuwar 'yan jam'iyyar Republican a majalisar dokokin kasar su nuna adawa da matakin, tunda dama can suna adawa da duk wani karin haraji bisa dalilin cewa hakan zai dakatar da zuba jari.

Haka kuma za'a sanya masa suna 'Buffett rule' wato ana alakanta shi na mai hannu da shuni wajen zuba jari, Warren Buffett wanda yayi korafin biyan karamin kaso na kudaden shigarsa a matsayin haraji, wanda bai kai abinda ma'aikata masu samun matsakaicin kudin shiga ke biya ba.