Sabon kwamanda a Jihar Filato

Wasu jami'an tsaro a jihar Filato Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu jami'an tsaro a jihar Filato

Rundunar sojan Nijeriya ta bayyana cewa tuni an fara tura karin dakaru zuwa jihar Filato mai yawan fama da rikici domin aiwatar da umarnin da shugaban kasar ya baiwa babban hafsan tsaron kasar na ya amshe ragamar tsaro a jihar.

Rundunar sojan dai yanzu ta nada sabon kwamanda, Manjo Janar Oluwaseun Olayinka Oshinowo,wanda zai jagoranci dukkkan rundunonin tsaro na kasar dake aiki a jihar ta Filato da nufin kawo karshen yawan zubda jini a jihar.

Kafin ba shi mukanin kwamandan rundunar a jihar ta Filato, Manjo Janar Oshinowo, shi ne daraktan sauye-sauye a hedikwatra tsaron Nijeriya dake abuja A wannan mako ne dai shugaban Nijeriyar ya umarci babban hafsan tsaron kasar, Air Marshal Oluseyi Petinrin, da ya yi iya kokarinsa domin ganin an maido da zaman lafiya a jihar.