An kammala taron 'yan adawa a Syria

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Syria

An kawo karshen wani babban taro na fitattun 'yan adawa fiye da dari biyu a kasar Syria, tare da yin kira da a kafa wata kungiyar hadaka ta- kasa da za ta kunshi dukkanin jam'iyyun dake adawa da shugaba Bashar Al Asad.

Hukumomi dai basu dakatar da taron ba amma sun sa ido sosai akan irin mutanen da suka halarci taron.

Taron ya bayyana cewa ya na adawa da bangaranci, da kuma tashin hankali, kuma basa son kasashen turai su tsoma masu baki a al'amuran kasar.

Wasu kananan kungiyoyin 'yan adawa basu halarci taron ba, saboda tsoron kada a kama su.