Girka na kokarin ceto tattalin arzikinta

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Girka ta ce idan ba ta samu tallafi ba, za ta tsiyace a watan gobe

Ministan kudin kasar Girka ya yi wata ganawar gaggawa ta sa'o'i biyu ta wayar tarho da wasu cibiyoyin da ke bada bashi na duniya, yayinda kasar ke fuskantar karin matsin lamba na kada ta gaza wajen biyan basussukan da ake binta.

Masu binciken kudi daga nahiyar Turai da asusun bada lamuni na duniya IMF suna nazari a kan shirin rage yawan basussukan gwamnatin Girkan.

Daga bisani za su yanke shawarar ko za su sakar ma ta karin kudi don ceto tattalin arzikinta.

Jami'ai sun ce za'a ci gaba da tattaunawar a gobe Talata.

Kasar ta Girka dai ta ce tana bukatar dala miliyan dubu goma sha daya don ceto tattalin arzikinta, ko kuma ta tsiyace nan da wata mai zuwa.