Nijeriya zata tura tawaga zuwa Libya

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta tura tawaga ta musamman kasar Libya don tattaunawa da gwamnatin rikon-kwayar kasar sakamakon rahotannin da take samu cewar sojojin `yan tawaye na musguna wa bakar-fata `yan ci-rani, cikinsu har da `yan Najeriya.

Wani binciken da BBC ta yi ya gano cewa ana washe gidajen bakar-fata `yan ci-rani, tare da yi wa matansu da `ya`yansu fyade, sakamakon zargin da ake musu cewar su sojojin-hayar gwamnatin Kanar Ghaddafi ne.

A baya dai gwamnatin Najeriya ta ce tana da fahimta da gwamnatin `yan Tawayen, don haka sojojinsu ba za su kuntata wa `ya Najeriyar ba.

Dr Nuruddeen Muhammad, minista a ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar, ya ce tuni an fara daukar matakan tura wannan tawaga zuwa birnin Tripoli.