Shirin Obama na rage bashin da ke kan Amurka

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama ya bayyana shirinsa na rage dimbin basussukan da ake bin Amurka, yana mai cewa dole ne kamfanoni da masu hannu da shuni a kasar su biya haraji mai yawa.

Da yake jawabi a fadar White House, Shugaba Obama ya ce kuskure ne a Amurka, malami ko ma'aikaciyar jinya, ko lebura da ke samun dala dubu hamsin a shekara ya biya haraji daidai da wanda ya ke samun dala miliyan hamsin.

Tuni dai shugabannin jam'iyyar Republican dake jan ragamar majalisar wakilan kasar su kai watsi da wannan shawara.

Sai dai Mr Obama ya ce zai hau kujerar na ki a kan duk wani kudurin da zai rage tallafi ga masu karamin karfi ba tare da ya kara haraji ga masu arziki ba.