Jami'an tsaro sun kashe mutane 25 a Yemen

Image caption Wani mai zanga-zangar da aka jikkata a Yemen

Jami'an tsaro a birnin Sana'a na Yemen sun bude wuta da manyan bindigogi akan dubban masu zanga-zangar kin jinin gwamnati, inda suka kashe akalla mutane ashirin da biyar.

Wasu shaidu sun ce jami'an tsaron sun yi amfani da makamai ta jiragen sama ne akan masu zanga-zanga a lokacin da suke kokarin danganawa da fadar shugaban kasar.

Wannan dai shi ne artabu mafi muni da aka taba gani a kasar a 'yan watannin nan.

Shugaba Ali Abdullah Saleh na kasar ya na Saudiya inda ake masa magani tun bayan mummunan raunin da aka ji masa a harin da aka kai fadarsa a watan Yunin da ya gabata.

Sai dai shugaban ya yi biris da kiraye-kirayen da ake yi masa kan ya sauka daga karagar mulki.