An rage darajar iya biyan bashin Italiya

Image caption Silvio Berlusconi

Daya daga cikin kamfanonin da ke auna karfin iya biyan basussuka na kasashen duniya ya rage karfin iya biyan bashin Italiya daga daraja mafi girma zuwa wacce ke kasa da ita.

Kamfanin na kasar Amurka, Standard and Poor's, ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan da ya yi la'akari da yanayin tattalin arzikin kasar.

Hakan na faruwa ne a yayin da ake fargabar yiwuwar sake fadawa cikin yanayin koma bayan tattalin arziki a kasashen Turai.

Duk da cewa majalisar dokokin Italiya ta amince da matakan tsuke-bakin-aljihun da gwamnatin kasar ta gabatar mata a makon jiya, kamfanin ya ce bambance-bambancen da ake samu a gwamnatin hadin-gwiwar kasar, sun sanya zai yi wahala gwamnati ta iya daukar kwararan matakan ceto tattalin arziki akan lokaci.