Hari kan kwamfutocin wasu kamfanonin Japan

Ma'aikatar tsaron kasar Japan ta nemi da a kara daukar tsauraran matsakan tsaro a katafaren kamfanin kera makamai na kasar, wato Mitsubishi Heavy Industries.

Hakan ya biyo bayan korafin da kamfanin ya yi cewa an shiga cikin kwamfutocinsa an yi masa barna.

Wani kamfanin kera makaman na biyu kuma mai suna IHI, ya ce ana ta aiko masa da sakwananin emails dake dauke da manhajar dake lalata kwamfuta.

Kamfanin Mitsubishi, wanda ke kera jiragen yaki na karkashin ruwa da makamai masu linzami da jiragen yaki na sama, ya ce an tura manhajar dake lalata kwamfuta cikin na'urorin kwamfutarsa a watan Agusta, amma ba wata alamar an saci wasu muhimman bayanai.