Bom ya kashe mutane 3 a Turkiyya

Bom ya kashe mutane 3 a Turkiyya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Motoci da dama sun kone a wurin da bom din ya tashi

Wani bom da ya tashi a tsakiyar birnin Ankara na kasar Turkiyya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu da dama.

Hayaki ya turnuke sararin samaniyar yankin kasuwanci na Kizilay inda motoci da dama suka kone.

Kurdawa da wasu kungiyoyin Islama sun sha kaddamar da hare-hare a Turkiyya a baya.

Wuta ta tashi na wani dan lokaci, amma masu aikin kashe gobara sun shawo kanta.

Motoci da dama ne suka lalace yayin da gilasan gine-gine suka farfashe.

Tuni dai 'yan sanda suka killace yankin.

Har yanzu dai mahukunta a kasar ba su ce ga takamai-man abin da ya fashe ba.