An bude taron Majalisar Dinkin Duniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Shugabannin kasashen duniya da suka taru New York na yin jawabi a wajen bude sabon babban taron Majalisar Dinkin Duniya. Ana saran taron zai maida hankali kan abubuwan dake faruwa a gabas ta tsakiya, da suka hada da rikice rikicen da akeyi a kasashen larabawa da kuma bukatar neman shigar Palasdin cikin mambobin Majalisar Dinkin Duniya da ake ta cece-kuce a kai. Palasdinawa sun ce wannan wani yunkurine na neman 'yanci da suka samu daga abinda ke faruwa a kasashen larabawa da kuma gazawar tattaunawar samar da zaman lafiyan da ake.

Shugaba Obama ya ce zai hau kujerar naki game da bukatar Palasdinu na neman shiga Majalisar Dinkin Duniya a madadin Isra'ila aminiyar Amurkan.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya lashi takobin yin kokari matuka domin samar da zaman lafiya tsakanain Isra'ila da Palastin ta hanyar tattaunawa.