Gwamnonin Arewacin Najeriya za su yi taro

Image caption Tutar Najeriya

A yau Laraba ne gwamnonin Arewacin Najeriya za su gudanar da taro a Abuja domin tattaunawa a kan al'amuran da suka shafi yankin.

Gwamnonin za su yi wannan taro ne a yayin da yankin ke fama da kalubalen tsaro, da koma bayan tattalin arziki, da tabarbarewar ilimi.

Wadansu 'yan kasar da suka yi tsokaci game da taron sun soki gwamnonin wajen gaza magance matsalolin da yankin ke fama da su.