Gwamnoni sun duba matsalar tsaro a arewacin Najeriya

Rikici a Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ko a wannan karon za ta sake zane?

A wani yunkuri dangane da yanayin tsaro a Najeriyia, musamman a arewacin kasar, a yau ne kungiyar gwamnonin jihohin arewacin kasar sun kammala taron wuni guda da suka yi a Abuja, babbban birnin Najeriya.

Sun dubadon duba hanyoyin da za a bi wajen shawo kan rigingimun, wadanda suka hada da rikicin Boko Haramm da kuma tashe-tashen hankula a jihar Filato.

Gwamnnonin sun bayyana cewa rigingimun da a yanzu suka fi kamari a wasu daga cikin jihohin idan ba a dauki mataki ba, to kuwa za su iya girma su game yankin baki daya.

Sun kuma amince cewa talauci na daga cikin abubuwan da ke haddasa rikice-rikicen, kuma sai an sama wa al`uma abin yi kafin a samu kwanciyar hankali.