Amurka za ta hau kujerar na-ki a kan bukatar Falasdinawa

Shugaba Barack Obama
Image caption Shugaba Sarkozy ya yi kiran samun sasantawa

Shugaba Obama ya shaida wa somin sabon zaman babban taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) cewa babu wata barauniyar hanya ta samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ana sa ran boren kasashen Larabawa da kuma bukatar Falasdinawa ta samun wakilci a matsayin cikakkiyar kasa a MDD, su ne za su kankane zaman.

To amma Mr Obama ya ce zaman ba za a samu zaman lafiya kawai ta hanyar sanarwa da kuma kudurori a MDD ba.

Amurka dai ta ce za ta hau kujerar na-k’i a kan bukatar Falasdinawan.

Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ma ya goyi bayan daidaitawa, inda ya yi tayin baiwa Falasdinawa matsayin ‘yan kallo a MDD.

Ya ce hawa kujerar na ki zai kara yawaita tashe-tashen hankula da ake yi a yankin gabas ta tsakiya.