Surukin Gaddafi yana hayar 'yan bindiga

Image caption Shugaban gwamnatin Libya, Mustafa Abdul Jalil

Wani kwamandan sojin majalisar wucin gadin Libya ya shaidawa BBC cewa surukin Kanar Gaddafi, Abdullah al-Senussi, na garin Sabha da ke kudancin kasar inda ya ke horasda sojojin haya domin su kare yankin.

Janaral Suleiman Mahmoud al-Obeidi ya ce wasu kabilu da ake ganin za su shiga cikin sojojin hayar sun tsallaka zuwa Libya daga Algeria a farkon wannan makon.

Garin na Sabha dai na daga cikin garuruwan da har yanzu magoya bayan Kanar Gaddafi ke iko da su, sai dai a 'yan kwanakin nan sojojin majalisar wucin gadin kasar sun kara matsawa zuwa kusa shi.

Janar Obeidi ya yi hira da BBC ne jim kadan bayan dawowarsa daga fagen daga a garin Sirte, mahaifar Kanar Gaddafi, inda anan ma ake fafatawa tsakanin dakarun gwamnati da na Gaddafin.