An zargi jami'an Pakistan da ta'addanci

Mike Mullen Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Admiral Mike Mullen

Hafsan Hafsoshin Sojin Amurka, Admiral Mike Mullen, ya ce kungiyar masu fafutuka ta Haqqani, wadda ta kai jerin hare-hare kwanan nan a Afghanistan, reshe ce ta hukumar ayyukan sirri ta Pakistan.

Admiral Mullen ya sheda wa 'yan majalisar dattijan Amurka cewa mayakan na Haqqani, sun shirya tare da kai hari a ofishin jakadan Amurka a birnin Kabul.

Admiral Mullen ya ce matakin Pakistan din yana yi mata zagon kasa ne ga matsayinta na siyasa a yankin.

Ya ce, "Za su iya dauka cewa ta yin amfani da wasu suna raba kafa ne, ko kuma daidaita abin da suke gani tamkar rashin daidaito a karfin juna yankin, amma a ainihin gaskiya an riga an tatuke su a wannan caca."

Ministan cikin gidan Pakistan din dai ya musanta zargin na Admiral Mullen.