Wasu yara sun mutu a Peru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Peru, Ollanta Humala

Wasu kananan yara uku sun mutu yayin da wasu guda shida suka kamu da rashin lafiya bayan da suka ci abincin da ya gurbace.

Abincin dai ya gurbata ne da maganin kashe kwari a wata makaranta.

Wani jami'in kiwon lafiya a kasar, Miguel Zumaeta, ya ce an dafa abincin ne a wata tukunyar da mai yiwuwa tana dauke da maganin kashe bera.

Fiye da mutane hamsin ne dai, wadanda suka hada da malami da kuma dalibansu, suka je asibiti don karbar magani bayan sun ci abincin ranar Talata.