Obama ya tattauna da Abbas

Image caption Obama da Abbas

Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da shugaban Palasdinawa, Mahmoud Abbas, inda ya jaddada kin amincewar Amurka na baiwa Palasdinawa kasar kansu.

Mr Obama ya ce hanyar kawai da Palasdinawa za su samu 'yanci ita ce ta hawa kan teburin shawarwari da Isra'ela.

Sai dai Mahmoud Abbas ya ce Palasdinawa za su ci gaba da yunkurinsu na samun kasa mai cin-gashin kanta duk da adawar da Amurka ke nunawa.

Isra'ela dai ta ji dadin matsayin da Amurka ta dauka na kin amincewa da kafa kasar Palasdinu.

Sai dai shugaban Faransa, Nicholas Sarkozy, ya ce rashin baiwa Palasdinawa kasar kansu zai iya kawo sababbin tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.