Ahmadinejad ya soki kasashen yamma

A jawabin da ya yi a Majalisar Dinkin Duniya, Shugaban Iran, Mahmoud Ahmedinejad, ya yi kakkausar suka kan kan manufofi da akidojin kasashen yamma, abin da ya sanya wakilai daga kasashe talatin da shidda suka fice daga dakin taron.

Shugaba Ahmedinejad ya ce kasashen masu izgili suna barazanar amfani da karfi a kan duk wanda ya bayyana kokanto a kan kisan Yahudawa da 'yan NAZI suka yi, ko kuma harin goma sha daya ga Satumba a Amurka.

Ya ce shekara sittin ke nan ana fakewa da batun kisan Yahudawan don tabbatar manufofin Yahudawan.