An gabatar da bukatar neman 'yancin Falasdinu

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas
Image caption Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce ba gudu ba ja da baya

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya gabatar da bukatar neman 'yancin yankin a matsayin cikakkiyar kasa ga Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.

Ya gabatar da wasikar neman kasancewa cikakkiyar mamba a Majalisar. Sannan kuma ya gabatar da jawabi ga babban taron Majalisar a birnin New York.

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai gabatar da nasa jawabin bayan Mr Abbas. Mai magana da yawunsa ya ce ya yi tur da matakin na Falasdinawa.

Isra'ila da Amurka na adawa da matakin, suna masu cewa za a cimma zaman lafiya ne kawai ta hanyar tattaunawa da Isra'ila.

Shugaba Barack Obama an Amurka ya gayawa Mr Abbas ranar Alhamis cewa Amurka za ta hau kujerar naki a kwamitin tsaro, amma Mr Abbas ya ce ba gudu ba ja da baya.

A gefe guda kuma, a yankin Yammacin kojin Jordan, Falasdinawa na yin maci domin ya dace da jawabin na Mr Abbas.

An sanya manyan allunan talabijin domin jama'a su samu damar kallon jawabin na Mahmud Abbas.

Mr Abbas ya nemi a yi maci cikin ruwan sanyi domin goyon bayan matakin na sa, amma an samu rahotannin tashin hankali.

Akalla Bafalatsi ne daya sojojin Isra'ila suka kashe lokacin da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna suka kai hari kan wata unguwa a garin Nablus.

Ya yi kira ga Isra'ila da su zo a zauna lafiya, sannan ya nemi a kawo karshen muzgunawa da cin zarafin da ake yi wa Falasdinawa.