Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Tsarin Iyali ta fuskar ma'aikatan lafiya

Image caption Wani likita na yiwa wata mata bayani kan tsarin iyali a Kenya

Tsarin iyali hanya ce da za ta baiwa iyali damar kayyade adadin yaran da suke so su haifa, ko kuma tazara tsakanin haihuwa ta hanyar amfani da wasu hanyoyin hana daukar ciki.

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta yi wani bincike da ke nuna cewa an samu karuwar adadin wadanda ke amfani da tsarin iyali na zamani, daga kashi uku da rabi cikin dari a shekarar 1990, zuwa kusan kashi goma cikin dari a shekarar 2008.

Sannan kuma an samu karin masu amfani da hanyoyin tsarin iyali na gargajiya daga kashi shida cikin dari a shekarar 1990 din zuwa fiye da kashi goma sha hudu cikin dari a shekarar 2008.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa tazara a tsakanin haihuwa na taimakawa matuka wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.

An buga misali da cewa a duk rana mata kimanin dubu daya da dari shida ne ke rasuwa yayinda jarirai fiye da dubu goma ke rasuwa a saboda matsalolin da suka danganci ciki ko haihuwa, wanda kuma hukumar ta ce hakan ya fi faruwa a kasashen da ke tasowa.

A wani bincike da fannin nazarin aikin likitanci na Jami'ar Ibadan ya yi game da amfani da tsarin iyali, ya gano cewa maza kimanin kashi 47 cikin dari na wadanda aka yi binciken akan su sun amince da cewa suna amfani da tsarin iyali.

Sai dai da dama daga cikinsu na ganin alhakin macen ne da ta dauki matakin tsarin iyalin akan kanta.

Sai dai kuma wannan wani nauyi ne da ya rataya ba wai akan mutum guda ba.

Shirin Haifi Ki Yaye da BBC Hausa na wannan makon, na dauke da cikakken bayani kan wannan lamari.