Isra'ila ta ce tana son zaman lafiya da Falasdinawa

Benjamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Benjamin Netanyahu

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya shaida wa Babban Taron Majlisar Dinkin Duniyar cewa yana mika hannun abota ga dukkan kasashen Gabas ta Tsakiya, amma musamman al'ummar Falasdinawa.

Sai dai ya ce za a iya cimma zaman lafiya na gaskiya ne kawai ta hanyar tattaunawar kai tsaye.

Ya yi kira ne a kan ci gaba da tattaunawa maimakon neman amincewa da kasar Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya.

Mr Netanyahu dai yana maida martani ne ga bukatar da shugaban Hukumar mulkin Falasdinawa, Mahmoud Abbas ya gabatarwa Majalisar ta neman cikakken wakilici a majalisar.