Palasdinawa na shirin gabatar da bukatar samun kasar kansu

Falasdinawa suna shirin yin taruka don su zo daidai da lokacin da Shugaba Mahmoud Abbas zai gabatar da bukatar Falasdinawa ta samun cikakken wakilcin kasar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya nan da 'yan sa'o'i.

Shugaba Abbas ya ce zai ci gaba da gabatar da wannan bukata, duk kuwa da cewa da Amurka ta yi za ta hau kujerar na-ki a kan bukatar Falasadinawan

Ran Falasdinawa dai bace yake game da matsayin da Amurkar ta dauka game da 'yancin Falasdinawan, kamar dai wannan mutumin a birnin Ramallah.

Ya ce, "Mun yi sassauci mai yawa a tattaunawa. Mun ba da abin da ya kai kashi saba'in da takwas cikin dari na kasar Falasdinu ta asali. Me kuma suke nema?"