Shugaba Abdallah Saleh na Yemen ya koma gida

Shugaba Ali Abdallah Saleh na Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Ali Abdallah Saleh na Yemen na koma kasar bayan ya shafe wata da watanni yana jinya a kasar saudi Arabiyya

Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh, ya koma kasar, bayan shafe watanni fiye da ukku yana jinya a wajen kasar sakamakon yunkurin halaka shi da aka yi.

Ya yi jinyar ce dai a kasar Saudi Arabia tun a watan Yuni, bayanda aka kai masa hari a harabar gidan shugaban kasa.

Shugaba Saleh dai, wanda ya shafe shekaru fiye da 30 yana mulkin kasar, yayi biris da zanga zangar da aka shafe wata da watanni ana yi, wadda tayi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

Komawarsa kasar na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar zanga zanga ta barke a Sana'a babban birnin kasar.